Ma’aikatar sojin tacea bara ne aka kama mutumin mai suna Kulbushan Jadhav a lardin Baluchistan.
Indiya ta tabbatar da cewar Jadhav tsohon jami’in sojan ruwan kasarta ne, sai dai ta musanta cewar yana gudanar da ayyukan leken asiri ne. Tace ya yi ritaya daga aikin sojin ne da wuri wuri.
Haka kuma hukumomin na Indiya sun karyata wani faifan bidiyo daaka nuna inda aka ce wai ya amsa laifin yin leken asirin, abinda hukumomin Indiya suka ce ba gaskiya ba ne.
Ya zuwa yanzu dai ba’a tsaida ranar aiwatar da hukuncin kisar ba.
Pakistan ta dade tana zargin Indiya da horarwa tare da bada taimakon kudi ga ‘yan bindiga masu shirya ta’addancin a boye a Baluchistan.
India da Pakistan abokan gaba ne da suka mallaki makaman nukiliya.
Kasashen biyu sun gwabza yake yake sau uku tun bayan lokacin da gwamnatin mulkin mallaka ta Birtaniya ta raba Pakistan da Indiya shekarar 1947 kuma har yanzu suna ci gaba da zaman dar dar da juna.
Facebook Forum