Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Amurka Da Na Afghanistan Sun Sami Nasarar Korar 'Yan Kungiyar ISIS


Sojojin Amurka da na Afghanistan dake gabashin kasar ta Afghanistan sun samu nasarar kakkabe ‘yan kungiyar ISIS daga wasu muhimmam wuraren da kungiyar take rike dasu tun a shekarar 2015.

Jami’ai da kuma mazauna wannan yankin ne suka shaidawa Muryar Amurka wannan batu.

Wakilin Muryar Amurka da ke kasar na Afganistan kuma yabi tawagar sojojin Afghanistan zuwa kauyuka dake yankin gundumar Achin, yace ya gane wa idanun sa yadda ‘yan kungiyar ta IS suka wargaza kauyuka.

Amma a tsawon kwanaki 10 da sojojin suka yi suna budewa ‘yan kungiyar ta IS wuta ba kakkautawa yasa a gabashin gundumar Nangahar, hakan yayi dalilin mutuwar ‘yan kungiyar ta IS masu yawan gaske, wannan yasa suna ji suna gani suka arce suka bar wadannan gine-ginen, kuma an lalata musu duk wasu abubuwan na jin dadi rayuwa.

Sama da gidaje 200 ne aka lalata, kana daruruwan iyalai ne suka bar muhallin su domin neman wani sabon matsugunni, kamar yadda wasu suka shaidawa wakilin na wannan gidan radiyon.

Daya daga cikin mazauna wuri yace mun bar gidajen mu domin mu tsira da rayuwar mu, inji Mohammed Anwar wani mazauni garin Anchin, yace gidajen mu duk an lalata su, ba abinda aka rage muna.

Da farko mazauna wannan wurin har sun fara fidda ran cewa sojojin na Afghanistan zasu iya shawo kan kungiyar ta IS.

Makarantu, kasuwanni, da sauran matattarar jama’a duk an lalata su, suka ce amma suna fata a sake gina su, domin jama’a su dawo kamar yadda Rahimullah wani mazauni daya daga cikin kauyukan ke cewa. Shimawani mazauni wannan wuri ya bayyana farin cikin sa yadda sojojin gwamnati ta samu damar fatattakar yan kungiyar ta ISIS.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG