Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Sake Mayar Da Dukkan Takunkumin MDD Kan Iran


Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo

Amurka mayar da dukkan takunkumin Majalisar Dinkin Duniya MDD kan kasar Iran, ciki har da takunkumin makamai kamar yadda wata sanarwa da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya fitar ranar Asabar.

Sanarwar ta kira Iran a matsayin babbar kasa a duniya dake taimakawa ta’addanci da nuna wariya ga Yahudawa, haka kuma sanarwar ta ce takunkumin za su fara aika daga daren ranar Asabar.

Amurka ta dauki wannan matakin ne saboda Iran ta kasa cika alkawuran da ta dauka karkashin yarjejeniyar JCPOA, kuma kwamitin tsaro na MDD ya ki daukar matakin tabbatar da ci gaban takunkumin makamai kan Iran wanda aka samar shekaru 13 da suka gabata, a cewar sanarwar.

Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif, ya amsa ranar Asabar ‘yan sa’o’i kafin Amurka ta sanar da shirinta na sake maido da takunkumin kan Iran.

“Amurkawa a matsayin mai zalunci da sanya takunmi… kamata ya yi al’ummar duniya su yi shawarar yadda za su dau mataki kan masu zalunci,” Zarif ya fadawa gidan talabijin mallakar kasar Iran.

Tun farkon mako, Pompeo ya gana da ministan harkokin wajen Birtaniya Dominic Raab a Washington. A wani taron manema labarai da suka gudanar ranar Laraba, Pompeo ya ce “Zamu koma MDD ta mayar da takunkumin saboda dokar makamai ta zamto ta dindindin a mako mai zuwa.”

Shi kuma Raab ya amsa da cewa “Ina tunanin mun amince cewa dole ne a hana Iran samun makaman Nukiliya.” Duk da haka, bai fadi ba ta yadda Birtaniya za ta tabbatar da aiwatar da takunkumin.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG