Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Umurnin Hana Amfani Da TikTok, WeChat a Amurka Na Gab Da Fara Aiki


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Ma’aikatar harkokin kasuwancin Amurka ta ce za ta fitar da wani umurni a ranar Juma’a wanda zai hana jama’ar kasar sauke manhajojin WeChat da TikTok na kasar China.

Umurnin zai fara aiki ne daga ranar 20 ga watan Satumba a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Jama’a na amfani da WeeChat ne domin aika sakonni yayin da suke amfani da TikTok domin aika hotunan bidiyo.

Sai dai hukumomin Amurka ba su aminta da manhajojin ba, domin ana fargabar za a iya satar bayanan jama’a.

Hukumomin ma’aikatar kasuwacin Amurka sun ce mai yiwuwa Shugaba Donald Trump ya soke umurnin haramta sauke sabuwar manhajar TikTok a Amurka kafin ya fara aiki a ranar Lahadi yayin da kamfanin da ya mallake shi ByteDance yake ta fadi tashin ganin an cimma wata matsaya kan makomar amfani da manhajar a Amurka.

Sai dai duk da haka, kamfanin na ByteDance na bukatar amincewar shugaba Trump kafin a dakatar da haramcin.

Kamfanin na ByteDance na ta tattaunawa da takwaran aikins na Amurka Oracle Corp da wasu kamfanoni don ganin yadda za a kafa wani sabon kamfani na hadin gwiwa a wani yunkuri na gamsar da Amurka kan fargabar da ta nuna.

Jami'an ma'aikatar sun ce sun dauki wannan mataki ne saboda kaucewa hadarin da ke tattara da manhajojin idan sun tashi karbar bayanan mutum.

China da kamfanonin sun musanta cewa ana karbar bayanan masu amfani da manhajojin a Amurka ne domin yin leken asiri.

Mutanen da ke amfani da TikTok a Amurka sun kai miliyan 100 kuma ya fi karbuwa a tsakanin matasa.

A daya gefen WeChat na da akalla mutum miliyan 19 da ke amfani da shi a Amurka a cewar wata kididdiga da kamfanin Apptopia ya yi a watan Agusta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG