Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ba Ta Saki Kari Ba A Kokarin Yin Katsalandan Ga Zaben Amurka


Daarektan FBI Christopher Wray
Daarektan FBI Christopher Wray

Bayanan binciken sirri na nuni da cewa har yanzu Rasha na kokarin yin kutse da katsalandan domin sauya sakamakon zaben Amurka na shekara ta 2020, kamar yadda ta yi a zaben shekara ta 2016.

A jiya Alhamis daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka - FBI, Christopher Wray, ya fadawa ‘yan majalisar dokoki cewa, Rasha ba ta ja da baya ba a kokarin sauya sakamakon zaben shugaban kasa na watan Nuwamba.

Wannan ya tabbatar da bayanan da hukumar tattara bayanan sirrin Amurka ta bayar a can baya cewa, babbar manufar Moscow shi ne ta lalata gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Democrat kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden.

Da yake ba da bahasi a gaban kwamitin tsaron cikin gida na majalisar, Wray ya kwatanta tasirin aikin Kremlin da cewa mai karfin gaske ne a kan shafukan sada zumunta da kafar yada labaranta da ma wasu hanyoyi da dama.

"Babban abin da Rasha take so ta cimma shine durkusar da mataimakin shugaban kasa Biden da kuma abin da Rasha din ke kallo a matsayin kin jininta," inji Wray.

Kalaman na daraktan hukumar ta FBI sun yi daidai da hasashen jama’a a farkon watan Agusta da ba a saba gani ba, game da barazanar da zaben Amurka ke fuskanta da babban jami’in hukumar leken asirin Amurka William Evanina ya bayyana.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG