Akwai yan gudun hijirar Venezuela kusan 250,000 da yanzu haka ke Brazil, yayin da kuma wasu 600 ke zuwa a kullum kafin a rufe iyaka saboda annobar coronavirus.
A wani taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Araujo, Pompeo ya ce “Yan gudun hijira suna son dukkan abin da dan Adam yake so, mutunci, suna son dimokaradiyya da zaman lafiya da kuma kiran Venezuela gida, inda su da iyalansu da ‘ya ‘yansu su sami aiki da kuma rayuwa cikin mutunci. Mu Amurkawa da Brazil muna goyon bayansu.”
Ya kara da cewa yayin da babu wanda ya san lokacin da Maduro zai sauka daga Mulki, “Ranar na nan zuwa.”
Pompeo ya sanar da cewa Amurka za ta bayar da dala miliyan $348 domin taimakawa ‘yan gudun hijirar Venezuela, ciki har da dala miliyan $30 ga ‘yan Venezuela dake kasar Brazil.
Facebook Forum