Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta nemi goyon bayan Saudiya akan yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria


Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yana ganawa da Sarki Salman na Saudiya
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yana ganawa da Sarki Salman na Saudiya

Jiya Lahadi sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya bukaci goyon bayan kasar Saudiya wajen karfafa yarjejeniyar rashin tsokanar fada tsakanin sojojin Syria da 'yan tawaye a kasar kafin taron da za'a yi wani lokaci a cikin wannan makon domin tattauna rikicin yankin.

John Kerry yana kokarin samun goyon bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ne a Syria wadda yanzu take tanga tanga.

Sakataren harkokin wajen na Amurka ya gana da Sarki Salman wanda kasarsa ke goyon bayan 'yan tawayen dake kokarin hambarar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad, shugaban kasar ta Syria.

Kamfanin dillancin labarun Saudiya ya bada rahoton cewa John Kerry ya tattauna da sarkin akan yadda al'amura suke a kasar ta Syria da takwaransa na kasar Abdel Al Jubair.

Bayan ya kammala ziyarsa a Saudiya jiya Lahadin John Kerry ya tashi zuwa Vienna inda shi da takwaransa na kasar Italiya zasu jagoranci taron ministocin harkokin waje akan matakan tsaro da kuma samarwa gwamnatin Libya goyon baya.

John Kerry da ministan harkokin wajen Saudiya Adel al-Jubeir
John Kerry da ministan harkokin wajen Saudiya Adel al-Jubeir

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG