Firaminista Cameron ya fada tun kafin ranar taron cewa, hakika cin hanci da rashawa makiyan samar da ci gaba ne, hakan ne yasa kasashe masu arziki irinsu Birtaniya da Amurka su amsawa duniya neman mafita.
Manufar taron shine, amincewa da duk dabarun fallasawa da kuma hukunta masu aikata wannan laifin a duniya. Taron zai hada da shugabannin Afghanistan, Colombia da kuma Najeriya.
A wani jawabi ga ‘yan jami’ar Oxford, Mista Kerry ya fadawa dalibai cewa, Amurka na nan tana aiki da Najeriya don yakar cin hanci da rashawa ba ji ba gani. Najeriya dai tana ji tana gani an fitar da Biliyoyin Daloli daga kasar cikin almundahana.
Kama daga kudaden bangaren harkar makarantu, harkar lafiya, ayyukan gwamnati da na sababbin ayyuka, aka fitar tare da boyewa a bankuna daban-daban dake kasashen duniya. Kerry yace ba ga kasashen masu tasowa kadai ba, har da masu arziki za a sawa idanu.