Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Aleppo dake kasar Syria ya batawa sakataren harkokin wajen Amurka rai


Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace ran shi ya baci kwarai saboda harin jirgin saman yaki da aka kai kan asibitin yara dake birnin Aleppo kasar Syria.

John Kerry bai bata lokaci ba ya dorawasojojin shugaba Bashar Al-Assad laifin kai wannan mugun harin da ya yi babbar barna.

Harin ya lalata asibitin da kungiyar likitoci ta na gari na kowa ko Doctors without boarders a turance dake lura da asibitin.

Akalla yara ishirin da likitoci ne aka kashe cikinsu har da wani likitan yara dake aiki a yankunan da suke hannun 'yan tawaye a Aleppo.

Mr. John Kerry ya yi kira ga Rasha babbar kawar Syria da ta yi anfani da tasirinta ta gayawa shugaba Assad ya kawo karshen kai irin wannan harin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG