A wata sanarwar da aka fidda bayan taron a Fadar Erga a can kasar, fadar White House tace, shugabannin sun tattauna kalubalen da Iran ke haifarwa yankin gabas ta tsakiya bisa takalar fada.
Amurka da Saudiyya sun lura da samun karuwar fargaba bisa yadda Iran din ke fuskantar al’amuran yaki da ‘yan ta’adda a yankin. Sanarwa tace Obama ya yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wutar rikicin Yamal, da kuma kokarin Sarkin Saudiyyar game ta kai kayan agaji a kasar.
Shugaba Obama ya sake jaddada muhimmancin sake aza kaimi wajen yakar ‘yan ta’addar ISIS, sannan ya yaba da rawar da Saudi ke takawa a cikin hadakar sojojin taron dangin da take jagoranta. Daga baya Obama ya gana da Yarima Sheikh Mohammed bin Zayed al- Nahyan na Abu Dhabi da Mataimakin babban kwamandan rudunar Sojojin hadaddiyar daular Larabawa.