Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya fitar da wasu jerin bukatu masu wuyar a iya aiwatar da su, wadanda da su za a yi amfani da su wajen cimma sabuwar matsaya kan shirin kera makaman nukiliya da Iran ke kokarin yi.
A jiya Litinin Pompeo ya fitar da jerin bukatun guda 12, yayin wani jawabi da ya gabatar a zauren wata gidauniya mai ra’ayin mazan jiya, wacce ita ta shimfidawa gwamnatin Trump wasu tsare-tsare, tun bayan da ta fice daga yarjejeniya ta nukiliya da Iran a farkon watan nan.
A cewar Pompoe, idan har za a sake kulla wata yarjejeniya, dole ne Iran ta yi watsi da duk wani aikin kera makamashin nukiliya tare da bai wa jami’an Majalisar Dinkin Duniya masu sa ido, damar ziyartar duk wani wuri da ake gudanar da shirin a kasar ta Iran.
Idan kuma har Iran din ba ta sauya akalar tafiyarta ba, a cewar Pompeo, “za a kakaba mata takunkumin matsin tattalin arziki da ba ta taba gani ba.”
Sai dai, shugaban Iran, Hassan Rouhani, ya yi watsi da wannan barzanar.
A wata sanarwa da ya fitar, wacce kafofin yada labaran kasar ta Iran suka wallafa a jiya Litinin, Rouhani ya ce: “wace ce Amurka da za ta rika fadawa Iran da Duniya abinda za su yi.”
Ya kara da cewa, “a yau ba Amurka ba ce take yankewa duniya shawara, domin kasashen suna da ‘yancin gashin kansu.”
Facebook Forum