Shugaban Amurka Donald Trump ya yiwa Iran kashedi a jiya Laraba yana mai cewa, Iran din ta kuka da kanta, idan ta fara kera makaman nukiliya, biyo bayan janyewar Amurka daga yarjejeniyar kasa da kasa ta shekarar 2015 da nufin takaita shirin nukiliyar Tehran din.
Shugaban na Amurka yayi wannan furucin ne a yayinda sauran kasashe biyar Jamus da Britaniya da Faransa da Rasha da kuma China, wadanda suma suka rattaba hannu akan yarjejeniyar suka baiyana goyon bayan ta.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya zanta da shugaban Iran Hassan Rouhani ta wayan tarho a jiya Laraba har na tsawon sama da awa guda
Shugaban Jamus Angela Merkel ta baiyana ficewar Amurka daga cikin yarjejeniyar abin takaici ta kuma ce Jamus zata yi iya bakin kokarinta ta tabbatar da ganin Iran ta cika alkawuran data yi nan gaba.
Tace ajiye yarjejeniyar da Trump ya yi, ya sake nuna musu cewar akwai babbar dawainiya a kansu a nahiyar Turai, game da manufofin kasashen waje a fannin samar da zaman lafiya da kuma fannin sasanta batutuwar siyasa.
Facebook Forum