Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da ministan tsaron Poland Mariusz Blaszczak sune suka sanya hannu a kan yarjejeniyar bayan takaitaccen jawabi daga shugaba Andrzej Duda.
“Amurka na mutunta kyakkyawar dangantakar mu da Poland. Muna zuba ido mu ga Poland ta amince da yarjejeniyar aiki tare, wanda zai bamu daman aiwatar da cikakken shirin inganta aikin hadin gwiwa na tsaro da shugabannin kasashen biyu da suka hada da Trump da Duda suka shirya, a cewar wata sanarwa daga ma’aikatar harkokin waje.
Yarjejeniyar, wani kari ne baya ga alakar su ta kungiyar tsaro ta NATO kana zata ba Amurka daman kafa karin sansanonin soja a kasar Poland.
Facebook Forum