Duk da matakan rage yawan ma’aikata da ayyuka, Evanston dake Chicago a jihar Illinois yana daukar matakan kaucewa fadiwar haraji na dala miliyan takwas zuwa miliyan 12 a cikin kasafin birnin na dala miliyan 117.
Kananan hukumomi suna daukar dawainiya masu yawa, daga gudanar da makarantun gundumomi da ayyukan ‘yan sanda da na ‘yan kwana-kwana domin samun ruwa a koda yaushe da kwasan shara da kuma gyare gyaren hanyoyi.
Ba kamar gwamnatin tarayya ba wacce ke karbo rancen triliyoyin dala domin gudanar da manyan ayyuka a shekara, su ko kananan hukumomi suna biyan ayyukan su daga kudaden da suka tara.
Shugaban Donald Trump ya aike da sakwanni daban daban na taimakawa kananan hukumomin. Watanni da dama ya nuna kin amincewar sa ga taimakawa garuruwa da jihohin da Democrat ke mulki bisa zargin su da rashin tattalin kudade. Sai dai a jiya Juma’a, shugaban kasar ya aike da wani sakon twitter cewa ya shirya ya aika da kudaden zuwa jihohi da kananan hukumomi, amma kuma yana zargin ‘yan Democrat a majalisar wakilai da jan kafa wurin tabbatar da kudurin.
Facebook Forum