Joe Biden, ya bayyana kafa babban tarihi, a yayin da yake gabatar da Sanata Kamala Harris, wadda ya zaba a zaman mataimakiyarsa a gangamin yakin neman zabe a Delaware.
Biden da Harris da dukan su suke sanye da takunkumin rufe fuska sakamakon annobar coronavirus, sun yi jawabai a dandalin taron a makarantar sakandaren garin Biden na haihuwa wato Wilmington.
Jawaban nasu sun mai da hankali ne akan taken yakin neman zabensu, suna masu jaddada cewa shugabancinsu zai taimakawa Amurkawa a lokutan annoba da ci gaban komadar tattalin arziki. Sun kuma bayyana hikimar da ke tattare da zaben Harris.
A hukumance Biden ya bayyana Harris a matsayin ‘yar takarar mataimakiyar shugaban kasa a jiya Talata, lamarin da ya sa ta zama mace bakar fata ta farko da aka baiwa wannan tikitin a babbar jam’iyya.
Biden ya ce shi da Harris za su aiki wajen "sake gina kasa."
Ya caccaki shugaba Donald Trump da mataimakinsa Mike Pence akan kasa shugabanci na gari a lokacin annobar COVID-19, inda ya ce shi da Harris za su gyara barnar da aka yi.
Facebook Forum