WASHINGTON, D.C. - Kamar yadda wani babban jami'in sojan Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press a ranar Laraba.
Gwamnatin mulkin soja ta Nijar ta kawo karshen wata yarjejeniya a watan da ya gabata wadda da ta bai wa sojojin Amurka damar gudanar da ayyukansu a kasar da ke yammacin Afirka.
Gwamnatin Chadi da ke makwabtaka da kasar a kwanakin baya ta kuma nuna shakku kan yarjejeniyar da ta kulla da Amurka, mataimakin shugaban hafsan hafsoshin tsaron kasar Adm. Christopher Grady, babban hafsan sojan kasar na biyu bada shiadan haka a wata hira da aka yi da shi.
Yarjejeniyar ta bai wa Amurka damar gudanar da muhimman ayyukan yaki da ta'addanci a cikin iyakokin kasashen kuma sun goyi bayan horar da abokan aikin soji a kasashen biyu. Juyayin da aka yi ya haifar da fargabar cewa tasirin da Amurka ke yi a Afirka abin tambaya ne inda Rasha da China suke samun fa’ida yanzu.
"Dukkanmu muna ƙoƙarin tabbatar da kanmu a matsayin abokin zaɓi," in ji Grady. "Ya rage namu mu nuna dalilin da yasa muke tunanin haɗin gwiwarmu da su yana da mahimmanci. Tabbas muna so mu kasance a wurin. Muna son taimaka musu, muna son karfafa su, muna son yin abubuwa a cikin su, tare da su."
Yayin da jami'an Amurka suka fada a ranar Asabar cewa sojojin za su fara shirin janye sojoji daga Nijar, sun ce ana ci gaba da tattaunawa kan wata sabuwar yarjejeniya ta soja.
"Har yanzu dai akwai tattaunawar da ake yi," in ji Grady. "Ban yi imani akwai yanke shawara ta ƙarshe game da kwashe sojojin Amurka a can ba."
-AP
Dandalin Mu Tattauna