Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Karfafa Pakistan Ta Daina Ba 'Yan Ta'adda Mafaka


 Nikki Haley, jakadiyar Amurka a MDD
Nikki Haley, jakadiyar Amurka a MDD

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ta fada cewa Amurka na karfafa gwuiwar Pakistan ta daina baiwa 'yan ta'adda makafa a kasar koina

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Nikki Haley ta fadi jiya Alhamis cewa Amurka na kara himma wajen karfafa ma kasar Pakistan gwiwa ta daina samar ko bada tundun mun tsira ga 'yan ta'adda ba.

Haley, wacce ke ziyara a kasar Indiya, ta ce kasar Pakistan na bayar da hadin kai, to amma Amurka ba za ta amince da duk wata gwamnatin da ke daure ma 'yan ta'adda gindi ba.

Hadin kan Pakistan na da muhimmanci ga manufofin Shugaban Amurka Donald Trump game da Afghanistan. Amurka na matsa lamba ma Pakistan kan ta daina bayar da mafaka ma 'yan ta'adda, wadanda ake zargi game da hare-haren da ake kai wa a Afghanistan. Kasar Pakistan dai ta karyata cewa ta na bayar da mafaka ga 'yan ta'adda, ta na mai jaddada cewa ana ruruta irin tasirin da ta ke da shi kan 'yan Taliban fiye da kima.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG