Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasuwannin Hannayen Jari a Turai da Amurka Sun Fadi


Shugaban Amurka Donald Trump wanda ya haddasa yakin cinikayya
Shugaban Amurka Donald Trump wanda ya haddasa yakin cinikayya

Rikicin kasuwanci dake tsakanin Amurka , Cina da kasashen Turai sanadiyar karin harajin da Amurka ta soma kafin sauran su soma mayar da martani ya jawo faduwar hannayen jari

Jiya Litinin kasuwanin hannaye jarri a turai da Amurka suka fadi a yayinda damuwa da ake nunawa akan rikicin kasuwanci yayi kamari a duk fadin duniya.

Kasuwar hanayen jarin Amurka ta fadi da wajen fiye da kashi daya daga cikin dari a yayinda kasuwanin hanaye jarri a turai suka fadi fiye da haka.

Anyi hasara to amma hanayen jarin fasaha su suka fi dandanawa domin sun fadi da fiye da kashi biyu daga cikin dari. Faduwa mafi girma da aka gani tun watan Afrilu.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bada sanarwar shirye shiryen kara kudin haraji akan kayayyaki da China ke sayarwa Amurka, yana misali da damuwa akan matakan tsaro.

Nan da makoni biyu Amurka ke shirin fara kara haraji akan kayayyakin da China ke sayar wa Amurka na fiye da dala biliyan talatin. China tayi alkawarin maida martini nan da nan, matakin daya sa kasashen na duniya guda biyu da suka fi kowace kasar bunkasar tattalin arziki fara rikicin kasuwanci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG