Majalisar Wakilai ta Amurka, ta yi watsi da gagarumin rinjaye da wata bukata wacce ta nemi da a yi wa tsarin shige da ficen kasar garanbawul, inda suka nuna halin ko-in-kula da magiyar da shugaba Donald Trump ya yi kan su amince da kudurin dokar.
Kuri’ar da aka kada a jiya Laraba, ta nuna cewa wadanda suka ki amincewa da kudirin sun samu kuri’u 301 yayin da wadanda suka zabi akasin hakan suka samu kuri’u 121, inda a bangaren ‘yan Democrat aka samu kwakkwaran hadin kai na adawa da kudurin, yayin da aka samu rarrabuwar kawuna a tsakanin ‘yan Republican.
Shugabannin ‘yan Republican sun amince da shi wannan kuduri, to amma da yawa daga cikin ‘yan gani-kashenin-jam’iyyar ta Republican, sun ki amincewa da kudurin, domin a cewarsu, hakan zai bai wa daruruwan dubban matasan bakin haure da ke zaune a nan Amurka, damar samun takardun iznin zama ‘yan kasa, wadanda a shekarun baya iyayensu suka shigo da su ba bisa ka’ida ba, lamarin da ‘yan adawan suka ce tamkar “afuwa” ne ga wadanda suka karya doka.
Wannan kaye` da kudurin ya sha, sharar fage ne ga aniyar shugaba Trump ta samar da wata kofa da za a fara aiwatar da dokar hana raba ‘ya’ya da iyayensu idan hukumomi suka kama su, a lokacin da suke kan tsallaka kan iyakar Mexico zuwa cikin Amurka ba bisa ka’ida ba.
Facebook Forum