Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Kautata Zaton Amurka Ta Hallaka Shugaban Taliban Na Pakistan


Janar Jim Mattis sakataren tsaron Amurka
Janar Jim Mattis sakataren tsaron Amurka

Wani hari da jirgin dake tuka kansa ya kai ya yi sanadiyar hallak Mullah Fazlullah shugaban Taliban na kasar Pakistan duk da cewa ma'aikatan tsaron Amurka ta ki ta ce komai a kai

Wani harin jirgi mara matuki da Amurka ta kai ya auna Shugaban Taliban a Pakistan a wani lardi a Afghanistan,wanda ke daura da kan iyakar Pakistan, abin da wani jami'in sojin Amurka ya tabbatar ma Muryar Amurka kenan. Wani rahoton da ya fito daga mazauna wurin, wanda ba a tabbatar ba, ya nuna cewa an hallaka Mullah Fazlullah.

Jami'in na sojin Amurka, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce harin, wanda aka kai da tsakar daren ranar Laraba, an auna shi ne kan Fazlullah, Shugaban Tehrik-e-Taliban, shiyyar Pakistan.

Zuwa yanzu dai jami'an Hedekwatar Tsaron Amurka sun ki cewa komai kan ko shin an yi nasara a harin ko a'a.

Jami'an na sojin Amurka sun ce Fazlullah ya bayar da umurnin kai wasu muggan hare-hare da dama kan muradun Amurka da Pakistan tun bayan da aka nada shi jagoran kungiyar a 2013, ciki har da hari kan makarantar soji ta Peshewar da ya yi sanadin mutuwar mutane 151, ciki har da yara sama da 130.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG