Shugaban Amurka Barack Obama tareda uwargidansa da ma'aikata a fadar White, sun tsaya tsit na wani dan lokaci da karfe tara saura minti 14 na safiyar yau, a dai dai lokacinda jirgi na farko ya kara da benen helkwatar hada-hadar kasuwanci ta Amurka dake New York. Anjuma da rana agogon Washington, Mr. Obama zai gana da sojoji da jami'an tsaro a wani taro na musamman a wani sansanin soji da ake kira FortMeade dake nan bayan garin Washington, domin yayi magana da Amurkawa dake suke aiki domin ci gaba da kare kasar.
A birnin New York, iyalan wadanda suka halaka a harin shekaru 14 da suka wuce, sun hallara a can inda za'a kada gwarji da kuma karanta sunayen wadanda suka halaka a harin.Anyi tsit na wani dan lokaci da karfe 9 saura minti 14, da kuma da karfe 9:03 lokacinda jirgi na biyu ya afkawa daya benen.
A Ma'aikatar tsaro ta Amurka da ake kira Pentagon, an gudanar da wani shiri a kebe domin iyalan wadanda suka rasa 'yan uwansu a harin da aka kai kan ma'aikatar. Daga bisani sakataren tsaro na Amurka Ashton Carter, zai jagoranci shirye shiye na musamman da rana.
Tunda farko yau an makala wata babbar tutar Amurka a bangaren ma'aikatar, inda jirgin saman da aka kawo harin dashi ya fada.