Sarauniyar Ingila Queen Elizabeth ta kafa tarihi a jiya Laraba, na bayyana kakar-kakarta a matsayin wacce ta fi dadewa a karagar mulkin sarautar kasar.
Ta bayyana haka ne a bainar jama’a lokacin da ake kaddamar da layin dogon na jirgin yankin Scotland na jirgin kasa tare da yin liyafar cin abincin dare a Balmoral Castle tare da yin bita.
Su kuma jaridun Birtaniya suna ta bayyana ita sarauniya a matsayin wacce taga abubuwa, kama daga hana cinikin bayi zuwa yakin cacar baka. Ta kuma ga mulkin Firayim ministocin Birtaniya guda 12 da shugabannin Amurka guda 12.
Ta shaida ganin mutuwar auren ‘ya’yanta guda 3 na bazata, da kuma shaida mutuwar tsohuwar sirikarta Princess Diana. Haka kuma tana da haihuwa da tattaba-kunnenta guda 2 da ke sahun gadon sarautar Birtaniya.
Sarauniya Elizabeth ‘yar shekaru 89 ta yabi Queen Victoria wadda da yi zamaninta na shekaru 63 da watannin 7 da ya kare a shekarar Alif 900 da 1.