Jiya Alhamis ministan harkokin wajen kasar Sin ko China ya bada sanarwar cewa kasar tana nazari akan rahoton dake cewa kungiyar ISIS ta cafke wani dan kasarta kuma tana garkuwa dashi.
Sanarwar ta ministan ta fito ne kwana bayan da kungiyar ISIS ta buga labarin cafke dan kasar China din cikin mujallarta ta yanar gizo. Ta nuna hotunan mutane biyu kuma tana neman a biyata diya da baya kayyade ko nawa ba ne kafin ta sakesu. Mutane biyun sun hada da Fan Jinghul dan shekara 50 da haifuwa daga Chinada kuma Ole Johan Grimsgaard-Ofstad dan shekara 48 da haifuwa daga kasarNorway.
Rahoton na ISIS bai fadi ranar da ta cafke mutanen da da wurin da ta samesu har ta kamasu.
Amma Firayim Ministan Norway Erna Solberg ya fada ranar Laraba cewa mahukuntar kasar sun ji kishin kishin cewa kungiyar ISIS ta cafke wani dan kasarta a Syria karshen watan Janairun wannan shekarar
Solberg yace kasarsa ta dauki duk matakan da suka kamata tare da yin anfani da iyawarta da manufar ana sako dan kasarta. To saidai ya hakikance gwamnatinsa ba zata biya 'yan ta'ada diya ba.