Hare-haren sun kaiga ruguza gine-gine biyu mafi tsawo a duniya dake birnin New York da aka sani da World Trade Center, wato cibiyar kasuwa ta duniya.
Harin ya shafi hekwatar ma'aikatan tsaron Amurka ta Pentagon da kuma wani fili a can jihar Pensylvania. Mutane fiye da dubu uku suka rasa rayukansu sannan manyan jiragen sama hudu na fasinjoji suka salwanta.
Yayinda a birnin Kansas ana shirin gudanar da sujadar tunawa da wannan ranar ta Satumba 11, 2001 a can jihar Florida kuma wani ya fada hannun 'yan leken asirin gwamnatin tarayyar Amurka da zargin cewa yana shirin kai harin bam yau din nan.
Ma'aikatar Shari'a tace wani dan shekara 20 mai suna Joshua Ryne Golberg ya yiwa wani da ban san dan leken asiri na FBI ba ne bayanan yadda ake sarafa bam da tukunyar pressure cooker. Irin bam din ne aka yi anfani dashi a harin shekarar 2013 a wurin tseren fanfaleke a birnin Boston wanda ya yi sanadiyar jikata mutane 264.
Golberg ya gayawa dan FBI din ya cika tukunyar da kusa da karafa da guban kashe bera ya kai ya ajiye a wurin da za'a yi sujadar tunawa da Satumba 11.
Idan aka tabbatar da laifin da ake zarginshi dashi to Golbert zai yi zaman gidan wakafi na shekara 20.
Yau birane da suka hada da Kansas zasu tuna da cika shekaru 14 da aka kawowa Amurka hari, wato ranar 11 ga watan Satumba na shekarar 2001. Harin ya hallaka mutane 3,000 a New York da Washington DC da kuma Shanksville dake cikin jihar Pennsylvania.