Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nukiliyar Iran - Yan Democrat Sun Hana A Kada Kura'a


Senate Minority Leader Harry Reid of Nevada, left, and Senate Minority Whip Richard Durbin of Illinois answer questions for reporters following the Senate vote on the Iran nuclear agreement on Capitol Hill in Washington, Sept. 10, 2015.
Senate Minority Leader Harry Reid of Nevada, left, and Senate Minority Whip Richard Durbin of Illinois answer questions for reporters following the Senate vote on the Iran nuclear agreement on Capitol Hill in Washington, Sept. 10, 2015.

A Majalisar dattijan Amurka wakilai 'yan Democrat sun hana majalisar kada kuri'ar nuna rashin amincewa kanyarjejneiyar da Amurka da wasu manyan kasashen duniya suka kulla da Iran, mataki da ya baiwa shugaban Amruka nasara ta fuskar harkokin difilomasiyya da kasashen waje.

Wakilai 42 'yan Democrat suka jefa kuri'a na hana jefa kuri'a nuna rashin amincewa da yarjejeniyar. Masu adawa da daidaiton sun gaza da kuriu biyu da zai sa a yi su kada kuri'a nuna rashin amincewa.
"Majalisar dattijai tayi magana da babban sauti inda ta ayyana cewa wannan yarjejeniya d a zata shiga tarihi wacce zata hana Iran kera makaman Nukiliya ya sami amincewa" inji Senata Harry Reid shugaban marasa rinjaye a majalisar, jim kadan bayan aka kada kuri'ar takawa 'yan Republican birki.
Da yake magana jim kadan bayan wannan mataki a majalisar dattjia, shugaban na AMurka Barack Obama yacewannan nasara ce ga tsarin difilomasiyya, ga tsaron Amurka da kuma zaman lafiya a duniya baki daya.
Amma shugaban masu rinjaye Mitch McConnell, wadanda aka kashewa guiwa yace, "yanzu senatoci 'yan jam'iyyar Democrat suka kada kuri'a na hana Amurkawa na kada kuri'a sahihi kan kuduri mai tasirin gaske gameda manufofin harkokin wajen Amurka.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG