‘Yan jam’iyar Republican a Majalisar Wakilan Amurka suna shirin kada kuri’a makon gobe kan wani kudurin dokar bakin hare ko da yake shugaba Trump ya gaya masu ranar jumm’a cewa, kada su amince da wannan yunkurin sai bayan zaben rabin wa’adi.
Koda ‘yan Jam’iyar Republican wadanda ke da rinjaye a majalisar wakilai da ta Dattawa sun amince da kudurin, kusan za a iya cewa babu ko tantama zai fuskanci matsala a majalisar Dattawa inda ‘yan jam’iyar Democrats suke da isassun kujerun takawa Republican birni, ta yadda ba zasu iya samun adadin kuri’u sittin da suke bukata na amaincewa da kudurin ba.
A farkon wannan makon, shugaba Trump ya yi kira ga majalisa ta gaggauta amincewa da dokar shige da fice. Sai dai ranar jumma’a ya buga a shafinsa na twitter cewa, “ya kamata ‘yan jam’iyar Republican su daina bata lokacinsu kan batun shige da fice sai bayan mun zabi Karin sanetoci maza da mata a watan Nuwamba. ‘yan Jam’iyar Democrat suna wasa ne kawai, basu da niyar yin wani abu domin shawo kan wannan matsalar da aka dade ana fama da ita. Zamu amince da kuduri mai kyau bayanda jar guguwa ta kada-inji shugaba Trump a sakonsa na twitter
Facebook Forum