Alkalin babbar kotun Amurka, ya ba gwamnatin kasar izinin sada bakin hauren da ta raba da ‘ya’yan su bayan sun ketara iyakar kasar, a wani bangare na farko da zai hana raba iyaye da ‘ya’yan su, har sai dai in iyayen basa iya kula da ‘ya’yan kokuma rayuwar yaran na cikin hatsari.
Alkalin kotun Amurka Dana Sabraw, ne ya bada umurnin a wata kara da kungiyar kare hakin bil’adama ta ta Amurka, ta shigar a madadin wasu iyalai da aka raba ta wajan kulle iyayen wuri daban da ‘ya’yan su.
Lamarin yayi sanadiyyar ware bakin haure sama da 2,300 da ‘ya’yan su watanni biyu daga lokacin da shugaba Donald Trump, ya bada umurnin ba sani ba sabo akan harkokin shigi da fice, da kudurin gurfanar da duk wanda ya ketara iyakar kasar ba bisa ka’ida ba.
Shugaba Trump, na ci gaba da korafi akan tsaurara matakan tsaro domin shiga kasar ta hanyar data dace.
Alkali Sabraw, ya bada odar hada yara ‘yan kasa da shekaru biyar da haihuwa da iyayen su cikin sati biyu, sauran masu matsakaitan shekaru kuma cikin wata guda.
Alkalin ya zargi gwamnatin Trump, wajan kafa dokar, inda ya ce, hukumomin gwamnati daban daban dake da al’haki akan tsaron iyakokin kasar basu shirya raba iyaye da ‘ya’yan su ba.
Facebook Forum