Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Twitter Ta Rufe Shafunan Mutane Dubu 125 Kan Laifin…………


FILE - A portrait of the Twitter logo in Ventura, California.
FILE - A portrait of the Twitter logo in Ventura, California.

Kamfanin sada zumunta na Twitter ya rufe shafunan mutane sama da dubu 125, dake da alaka da ayyukan ta’addanci tun tsakiyar shekara ta 2015, yawancin shafunan na da alaka da kungiyar ISIS a cewar kamafanin.

Twitter tace tana rufe shafunan ne bayan da sauran masu amfani da shafin sada zumuntar suka ankarar da ita kan abinda yake faruwa, amma yanzu kamfanin yace ya kara kaimi wajen kula da kuma binciken duk wasu kalamai da suka shafi aikin ta’addanci.

Wannan sanarwa ta Twitter ta zo ne bayan da duk sauran kamfanonin sada zumunta na kan yanar gizo, karkashin jagorancin Facebook suka kudiri aniyar taimakawa jami’ai da duk wani bayani da ya shafi barazanar ta’addanci, alokacin da ‘yan majalisu ke kokarin tilastawa duk kamfanoni da su sanarwa jami’an tsaro.

Kamfanonin sadarwa na jan baya wajen aiki tare da jami’an tsaro, hakan ya kara musu damuwa kansancewar sauran kasashen duniya ma na bukatar su da baiwa jami’ai hadin kai, damuwar kanfanonin anan itace kar shafunan su zamanto wani kayan aikin gwamnati mai makon na jama’a.

XS
SM
MD
LG