Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakacin Dan Adam Na Kara Tsananin Bala'o'i Daga Allah


Libya Floods
Libya Floods

Matsalar shugabancin da Libiya ta ke fuskanta inda bangarori biyu masu adawa ke iko da yankunan kasar, ta haifar da rikicin cikin gida wanda ya gurgunta harkokin tanadin ko ta kwana.

Wani rukunin masana kimiyya ya bayyana cewa sauyin yanayi a sakamakon al'amuran dan adam ya yi tasiri wajen ta’azara matsalar ambaliyar ruwan da ta auku a gabashin Libya a farkon watan nan.

Bisa ga rahoton wani sabon bincike da kungiyar WORLD WEATHER ATTRIBUTION ta fitar a jiya Talata, ana kyautata tsammanin cewa, kaso 50 cikin 100 na dumamar yanayin da duniya take fuskanta yayi tasiri kan aukuwar ambaliyar.

Da yammacin ranar Litinin ne MDD ta sake nazarin alkaluman mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan na Libya, kana, ta kuma sheda cewa addadin wadanda suka mutu ya zarce 3,900 sannan har yanzu ba a gano sama da mutum dubu 9,000 ba

Shugabannin Libya sun karkasa birnin Derna gida 4 domin samun saukin cunkoso wajen bada kulawar matakan kariya a daidai sa’adda kungiyoyin MDD su ke fargabar samun yaduwar cututtuka a fadin birnin da zai iya haifar da wata sabuwar matsalar jinkai ta biyu.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a Birnin na gabashin Libyan bayan da mahaukaciyar guguwar nan mai lakabin Daniels ta kado, ya haifar cikar ruwan wasu madatsun ruwa biyu da aka gina a shekarun alib dari tara da saba’in, lamarin da ya sa suka tumbatsa sannan ruwan ya malale birnin wanda ya yi gaba da gidaje.

A Mediterranean city known for hills, valleys and beautiful views, Derna, Libya, residents say their city may never recover from the floods that killed thousands last week, pictured on Sept. 17, 2023.
A Mediterranean city known for hills, valleys and beautiful views, Derna, Libya, residents say their city may never recover from the floods that killed thousands last week, pictured on Sept. 17, 2023.

Caitlin Grady, farfesa ce a fannin kimiyyar kere-kere a jami’ar George Washington da ke Amurka. Grady tana nazarin mu’amala tsakanin kayakin more rayuwa da abinci da tsarin samar da makamashi. Sannan fannin da Grady ta kware akai ya hada da yadda za a iya daidaita al’amuran sauyin yanayi, da kuma yadda sauyin yanayi yake shafar samar da wutar lantarki da samar da lantarki a Amurka da kuma yadda za a shawo kan matsalolin da aka tsinci kai ciki. Binciken nata yana nazari kan yiwuwar yadda za a hada tsarin sadarwa, da bayanan kimiyyar zamantakewa.

A cewar Grady, ruwan da akayi mai karfi da kuma fashewar madatsun ruwa a Libya, wani lamari ne da zai tunutar da mutane cewa sannu a hankali, bala’o’i daga Allah suna kai ga haifar da bala’o’in da dan Adam ya yi sanadinsu a dalilin sakaci. Wannan kuma zai fargar da mu cewa zamu iya daidaita ayyukanmu da matsalolin sauyin yanayi ta yadda bala’o’in yanayi ba za su dogara kawai da abin da illimi ya sanar da mu ba amma abubuwa kamar siyasa, mu’amalar mu, da kuma tattalin arziki suma za su yi tasiri a bangaren samar da abubuwan more rayuwa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG