Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sama Da Mutane 100 Sun Mutu A Arewacin Indiya Sanadiyar Ambaliyar Ruwa


Himachal Pradesh, India
Himachal Pradesh, India

Wani ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya sauka a Arewacin Indiya ya sa an rufe makarantu da kwalejoji, ya kuma haifar da taruwar ruwa a wurare da dama, rugujewar gidaje da cunkoson ababen hawa, wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 100 cikin makonni biyu, in ji jami'ai a ranar Alhamis

WASHINGTON, D.C. -Akalla mutane 88 ne suka mutu, 42 daga cikinsu a cikin kwanaki biyar da suka gabata, yayin da fiye da 100 suka jikkata a jihar Himachal Pradesh wadda ta fi fama da rikici, inda tsananin ruwan ya yi ambaliyar da ta yi awon gaba da kananan motoci, da motocin safa, da gadoji da gidaje, in ji sanarwar gwamnatin jihar. Yankin yana kusan kilomita 500 (mil 310) ne arewa da New Delhi.

Wasu karin mutane 12 kuma sun mutu sakamakon abubuwan dake da alaka da ruwan saman tun ranar Laraba a jihar Uttar Pradesh, in ji Shishir Singh, kakakin gwamnatin jihar.

Hukumomin kasar sun yi amfani da jirage masu saukar ungulu wajen ceton kusan mutane 300 galibi ‘yan yawon bude ido da suka makale a yankin na Chandertal da ke jihar Himachal Pradesh tun ranar Asabar. Sun hada da majinyata bakwai da aka kwashe a ranar Talata, in ji gwamnati.

Madatsar ruwan kogin Jamuna da ke ratsa babban birnin Indiya a yanzu haka ta cika ta batse irin da ba a taba gani ba a cikin shekaru 40 a tarihi, inda kuma ya kai mita 207.71 (kafa 681.5) a yammacin Laraba, a cewar wata sanarwa da ofishin babban zababben jami'in New Delhi, Arvind Kejriwal ya fitar.

Hukumar kula da yanayi ta Indiya ta yi hasashen za a sake samun karin ruwan sama a sassan Arewacin kasar a cikin kwanaki masu zuwa. Ta ce ruwan saman damina na Monsoon a fadin kasar ya riga ya sauke sama da kashi 2% fiye da yadda aka saba.

Indiya a kai a kai tana fuskantar mummunar ambaliyar ruwa a lokacin damina, wanda ke gudana tsakanin watannin Yuni da Satumba wanda ya kan kawo yawancin ruwan sama na Kudancin Asiya. Ruwan sama na da matukar muhimmanci ga amfanin gonakin da ake shukawa a lokacin damina amma yakan haifar da barna mai yawa.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG