Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa: Buhari, Atiku, Kwankwaso Sun Jajanta wa Al’umar Maiduguri


Yadda wasu gidaje suka nutse a ambaliyar ruwan Maiduguri
Yadda wasu gidaje suka nutse a ambaliyar ruwan Maiduguri

Tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso sun jajanta wa al’umar jihar Borno bisa ibtila’in ambaliyar ruwa da ta auka wa birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Da tsakar daren Litinin wayewar garin Talata ambaliyar ruwa ta malale wasu yankunan babban birnin na Borno bayan da wani sashe na madatsar ruwan Alau ya fashe.

Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa dangane da wannan al’amari yana mai fatan hukumomin agaji za şu taimaka wajen saukaka radadin ambaliyar.

“Tunaninmu da addu’oi’nmu suna tare da wadanda wannan ibtila’i ya shafa.” Buhari ya ce çıkın wata sanarwa da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar.

Shi mai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya mika sakon jajensa.

“Zuciyarmu tana tare da al’umar Maiduguri da gwamnatin jihar Borno yayın da suke fama da wannan babbar jarabawa da ta shafi tattalin arziki” Atiku ya ce cikin wata sanarwa da ya fitar a kafafen sada zumunta.

Ya kara da cewa, “ina kuma kira ga hukumomin ba da agaji da su gaggauta kai dauki don saukakawa jama’a wannan bala’i.”

A nasa bangaren, tsohon gwamnan Kano Kwankwaso ya ce, “Ina kira ga hukumomi da dukkan wadanda za şu iya taimakawa da şu kai wa jama’a dauki.”

“Tunaninmu da addu’inmu na tare da gwamnatin jihar Borno da al’umominta yayin da suke fuskantar wannan mawuyacin hali.’ Kwankwaso ya kara da cewa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG