Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa A Maiduguri Ta Janyo Arcewar Fursunoni


Ambaliyar Ruwa A Maiduguri
Ambaliyar Ruwa A Maiduguri

Ambaliyar ruwa ta rusa katangar gidan yarin Maiduguri dake yankin “Custom” inda wasu fursunoni suka nutse sannan wasu da dama suka arce domin neman tsira da rayukansu.

Ambaliyar ta mamaye manyan hanyoyi da shaguna a birnin maiduguri, fadar gwamnatin jihar borno da wani yanki na karamar hukumar Jere.

Fadar Shehun Borno da asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri da gidan namun daji na sanda kyarimi na daga cikin gine-ginen gwamnati da ambaliyar ta malale.

Dubban mazauna yankin dake kusa da gangare da yankunan fadama sun rasa muhallansu, kuma galibinsu mata ne da kananan yara.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG