Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Allah Yayima Mal. Abubakar Ladan Zariya Rasuwa


Mal. Abubakar Ladan Zariya
Mal. Abubakar Ladan Zariya

Anyi jana'izar rasuwar Mal. Abubakar Ladan Zariya.

Inna-Lillahi Wa-inna Ilaihi raji'un. Daga Allah muka zo kuma gare shi zamu koma. Allah yayi ma Mal. Abubakar Ladan Zariya rasuwa, jiya a mahaifar shi Zariya. bayan wata jinya da yayi. Mal. Abubakar Ladan, wani sannanen marubuci ne wanda ya shahara wajen rubuta wakoki, akan zaman lafia da son juna.

A kiyasin da akayi Mal. Abubakar Ladan yakai shekaru 81 zuwa 82 a rayuwarshi ta duniya. Dr. Aliyu Tilde, ya bamu takaitaciyyar tarihin rayuwa mamacin, ya shaida mun cewar Mal. Abubakar yayi karatu shin na elemetary da kuma sakandire duk a zariya wanda yana cikin karatunshi na sakandire ya bari yashiga yawon duniya, ya je kasashen Afrika da dama, wanda daga bisani ya rubuta wakarshi ta Afrikiya a shekarar 1962. Ya dai mutu yabar mata daya da kuma ‘yaya goma sha daya (11).

Allah Yayima Mal. Abubakar Ladan Zariya Rasuwa - 4'09"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:09 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG