Bayanai dake fitowa daga yankin Ibi sun nuna cewa wasu dauke da bindigogi suka yi kwantar bauna akan hanyar Wukari zuwa Ibi.
Wasu matafiya a cikin mota sun gamu da ajalinsu yayin da suka kai inda 'yanbindigan suka buya. Nan take suka budewa matafiyan wuta lamarin da ya kai ga asarar rayuka. Saidai har yanzu ba'a gano wadanda suka kai harin ba balantana a san manufarsu.
Masu lura da alamuran dake faruwa a yankin sun ce harin yayi kama da irin wanda kabilun yankin ke kaiwa junansu. Wani ganao yace wani direba Alhaji Danladi Bagauda ta yi lodin mutane daga Wukari zai tafi Jalingo. A cikin motar akwai mata da yara dukansu 'yanbindigar suka kashesu sai mutum daya ne ko biyu suka tsira da ransu. Yace idan bahaushe yana tafiya aka harbeshi to an san wanda ya kasheshi.
Cikin kwanakin nan an sha samun hare-hare lamarin dake tada hankalin mutanen yankin. Alhaji Abdullahi A Ibrahim Dan Masanin Garin Ibi yana cikin wadanda suka rasa 'yanuwa a cikin kwantar baunanda aka yi. Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kai masu doki. Yace a sa sojoji a kan hanyar su taimaka.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.