Kimanin marayu dubu bakwai ne suka samu tallafin na gudurmawar kayan Sallah a jihar Neja, dake tsakiyar Najeriya, kungiyar Izala ne ta bada gudurmawar kayan da suka hada da Tufafi da kayan abinci.
Manufa dai shine taimakawa marayun domin suma su gudanar da shagalin Sallah kamar yadda duk wani yaro mai iyaye zai gudanar cikin kwanciyar hankali.
Sheikh Aliyu Adarawa, shugaban majalisar Malaman Izala, a jihar Neja, yace kungiyar ta kashe kimanin Naira miliyan goma wajen siyan kayayyakin tallafin, ya kara da cewa “Allah subahanahu Wata’ala yayi alkawarin duk wanda ya tausayawa mai rauni Allah zai taimakamasa, wanda kuma ya taimakawa maraya Allah zai taimakeshi kuma ya taimakawa na bayan shi.”
Kungiyar tace tun a shekara ta 2006, ne ta fara wannan aiki na baiwa marayun tallafin kayan Sallaha jihar Neja, inda kawo yanzu haka ta kashe sama da Naira milyan ashirin da daya akan wannan aikin.