A yayin da ake shirin fara aikin haji gadan gadan a gobe litinin hukumar alhazzan jamhuriyar Nijer da kamfanin jigila na Max Air sun sanar da kammala kwashe illahirin maniyatan kasar dai dai da kason da hukumomin Saudia suka ware wa Nijer a shekarar nan ta 2023, abin da ke nufin an yi nasarar magance dadaddiyar matsalar jigilar alahazzai da ake fuskanta a baya.
A yayinda yake bitar karshen aiyukan jigilar maniyata zuwa kasa mai tsarki a albarkacin hajin shekarar 1444 da ke dai dai da shekarar mai ladiya ta 2023 shugaban hukumar alhazzan Nijer Commissaire Ibrahim Kaigama ya tabbatar da cewa an yi nasarar isar da dukkan maniyatan kasar akan lokaci.
Kamfanin MAX Air na daga cikin kamfanoni 3 da suka yi aikin jigilar alhazzan Nijer a bana. Ganin yadda abubuwa suka wakana ba tare da wata babbar tangarda ba ya sa wakilin kamfanin a wannan kasa Dan Majalissa Alhaji Boukari Sani Zilly yin hamdala saboda babbar rawar da MAX Air ya taka a kokarin warware matsalar dakon maniyan haji inji shi.
Sai dai zancen nan da ake akwai wasu maniyatan da alamu ke nunin ba zasu sami tafiya kasar Saudi ba a bana sanadiyar rashin samun takardar Visa. Lamarin da ke da nasaba da rashin adalcin wasu daga cikin ejoji.
A nan dan majalissar dokokin kasa Boukari Sani Zilly ya shawarci hukumar alhazzai ta COHO da ma gwamnatin Nijer da kanta su dauki matakai don kara tsaftace sha’anin haji.
Rashin kamfanin jigilar jiragen sama mallakar gwamnati ko na wasu ‘yan kasuwar cikin gida ya sa a kowace shekara mahukuntan Nijer ke bayar da kwangilar jigilar maniyatan kasar ga kamfanonin kasashen waje.
A ‘yan shekarun nan kamfanin MAX Air na attajirin Najeriya Dahirou Mangal ne samun wannan aiki sai dai wasu ‘yan kasa na sukar wannan haraka da suke dangantawa da dalilai masu nasaba da siyasa mafari kenan a bana aka shigo da Ethiopian Air Lines da Fly Nas na Saudi. Abin jira shine dawowar alhazzan na Nijer akan lokaci bayan kammala aikin hajin bana.
Saurari rahoton a sauti: