Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummomi Dake Zaune Kan Iyakokin Nijar Da Najeriya Na Neman Karin Tsaro


Wasu al'ummomi dake  kananan hukumomin Illela da Gudu
Wasu al'ummomi dake  kananan hukumomin Illela da Gudu

A Najeriya al'ummomi dake zaune akan iyakokin kasar sun jaddada kira akan karin jami’an tsaro a yankunan don taimakawa ga dakile ayukkan 'yan bindiga wadanda ke haddabar yankunan.

Wannan na zuwa ne lokacin da aka yi Jana’izar mutane goma da ‘yan bindiga suka hallaka a kananan hukumomi biyu dake Sakkwato wadanda ke makwabtaka da jamhuriyar Nijar.

Matsalar rashin tsaro dai na ci gaba da addabar ‘yan Najeriya musamman a yankin arewa duk da yake hukumomi suma suna kokarin ganin sun dakile ayukkan na ‘yan bindiga.

A jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya al'ummomi dake kananan hukumomin Illela da Gudu garuruwan da dukan su sun yi iyaka da Jamhuriyar Nijar na ci gaba da zaman dar-dar domin ‘yan bindiga na ci gaba da yi musu barazana.

Shugaban karamar hukumar Illela Injiniya Aliyu Salihu yace ko a jiya Alhamis sai da suka yi janaizar Mugabe biyar da ‘yan bindiga suka hallaka a wani kauye.

A yankin Gudu dake arewa maso yammacin jihar, wanda kuma yayi iyaka da Jamhuriyar Nijar ‘yan bindiga suna ci gaba da haddabar jama'a.

Shugaban karamar hukumar Bello Wakili Bachaka yace a kwanannan ma ‘yan bindiga sun yi artabu da ‘yan banga inda suka kashe ‘yan bangar uku, kuma suka sace mutanen gari biyar.

Bisa hakan ne jagororin al'ummomin ke jaddada kira akan karin jami'an tsaro da kuma kara basu kayan aiki a fafatawar da suke yi da ‘yan bindigar.

Duk kokarin jin ta bakin jami'an tsaro akan wadannan hare haren a Illela da Gudu ya ci tura.

Dama masana lamurran tsaro sun jima suna shawartar mahukumta akan abubuwan da suka shafi samar da tsaro wadanda da ana amfani dasu da watakila an samu saukin wadannan matsalolin.

‘Yan Najeriya dai na cike da gurin ganin lokacin da lamarin rashin tsaro zai kawo karshe koda lamurran yau da kullum zasu gudana cikin sauki da walwala.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG