Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Uku A Garin Illelah Mai Iyaka Da Jamhuriyar Nijar 


‘Yan Bindiga
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:12 0:00

Wasu 'yan fashin daji a Najeriya.

Wannan lamarin ya zo ne a daidai lokacin da a ke tunanin cewa, kura ta lafa a wannan garin na Illela.

Wadansu ‘yan bindiga dauke makamai sun afkawa jama'a a karamar hukumar Illela Local ta jihar Sokoto da ke tazarar kilomita uku kawai da Birni N'Konni na Jamhuriyar Nijer inda suka kashe mutane uku suka kuma tafi da wadansu mutane uku ciki hadda mace daya.

Wadansu mahara ne da ba a san ta daga ina suka bullo ba, dauke da makamai sun budewa wadansu bayin Allah wuta a karamar hukumar Illela da ke arewa maso gabashin jihar Sokoton Tarrayar Najeria dake kan iyaka da Birni N'Konni a Jamhuriyar Nijar.

Abin dai ya faru ne da maraice kafin a kwanta bacci duk da yake lokacin sanyin hunturu ne.

Daya daga cikin ‘yan uwan wadanda wannan lamarin ya rutsa da su, da muka sakaye sunan sa saboda dalilai na tsaro ya tabbatarwa da Muryar Amurka aukuwar wannan lamari.

Wannan lamarin ya zo ne a daidai lokacin da a ke tunanin cewa, kura ta lafa a wannan garin na Illela, kasancewa an dade ba'a samu irin wannan hari ba na abkawa jama'a tun makwanni da dama da suka shude, a lokacin da jama'ar garin sukayi gaba da gaba da yan bindiga har ma suka gama da mai tsegumi wa maharan.

‘Yan uwan wadanda abin ya rutsa da su a cikin garin Illela sun yi kira ga hukumomin Najeriya da sukai musu dauki.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG