Shaidun gani da ido sun ce mayakan sakan ‘yan kungiyar da take kiran kanta kasar Iraqi da Syria masu bin tafarkin Islama, ko ISIS a takaice, sun yanke wutan lantarki a birnin suka kuma umarci mazauna yankin kada su yi amfani da janareta.
Amma baturen ‘Yansanda na binrin Fallujah Mohammed al-Isawi, ya karyata ikirarin mayakan cewa su suke rike da birnin, a hira da jaridar New York Times, baturen ‘Yansandan yace ya girke jami’ans a daga arewacin birnin domin shirin karon batta.
Yace dakarunsa sun sami goyon bayan shugabannin kabilu, kuma tuni har sun kwace wani bangaren birnin a daren jiya.
Wani dan jarida a kasar wanda ya nemi a sakaye sunansa ya gayawa jaridar Washington Post cewa ‘Yansanda da wasu jami’an gwamnati duk sun gudu, kuma ‘yan al-Qaidan sun kona duk tutocin Iraqi.
Fada da ake gwabzawa a yammacin kasar ya zamo zakaran gwajin dafin karfin PM kasar Nouri al-Maliki na ci gaba da hade kan kasar lamari d a zai hana barkewar yakin basasa gadan gadan.