Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarihin Rayuwar Osama Bin Laden


This video frame grab, obtained from ABC News on May 2, 2011, shows the interior bedroom in the mansion where Osama Bin Laden was killed May 1.
This video frame grab, obtained from ABC News on May 2, 2011, shows the interior bedroom in the mansion where Osama Bin Laden was killed May 1.

Osama Bin Laden, haifaffen kasar Saudi Arebiya ne, an kashe shi yana da shekaru hamsin da uku da haihuwa. An kashe shi a daren lahadi daya ga watan Mayun shekarar miladiyya 2011, an kashe shi ne a kasar Pakistan.

Ana zargin marigayi Osama Bin Laden da laifin shiryawa da kafa kungiyar ta’addanci ta al-qaida. Ana kuma zargin Osama Bin laden da laifin kai hare-haren ta’addanci kan sassa daban-dabam a duniya. A tarihin Amurka babu mutumin da tafi maida hankali wajen farautarsa a duniya irin Osama Bin Laden. Duk kuma abinda ya janyo haka shine jagorancin da Osama Bin Laden yayi wajen kai hare-haren ta’addanci a New York cibiyar cinikayyar Amurka a ran sha daya ga watan Satumban shekarar miladiyya 2001. Bayan harin ne shugaba Bush ya fito fili a bainar jama’a yayi rantsuwar sai ya kamoshi ya gurfana gaban shari’a.
An haifi Osama Bin Laden a ran goma ga watan Maris shekarar miladiyya 1957. Osama Bin Laden, shine da na hamsin a waajen iyayensa wadanda attajirai ne a kasar Saudi Arebiya.Osama Bin Laden ya fara samun chanji rayuwa ne daga shekarar 1979 lokacin da yaje ya shiga rundunar sojin “mujahedin” domin yakar sojin tsohuwar tarayyar Soviet da suka mamaye kasar Afghanistan.Ita wannan kungiyar ta Mujahedin, ta sami cikakken goyon bayan Amurka. A shekarar 1980 kuma ya koma gida domin samun isassaun kudin da ya kafa tasa kungiyar ‘yan jihadi tasa ta kansa, kungiyar da daga bisani aka sa mata sunan “al-Qaida.”


XS
SM
MD
LG