Fadar Shugaban Najeriya ta mayar da martani, dangane da abin da ta kira yunkuri da wasu ke yi na ganin sun sauya gwamnatin kasar.
Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan sha’anin yada labarai, Femi Adesina, ya yi zargin cewa, wasu shugabannin addini da tsoffin shugabannin kasar na kokarin ganin an sauya gwamnatin Buhari ta kowane hali.
Adesina ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, wacce ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Cikin sanarwar, kakakin Shugaban ya zargi wasu mutane “da kokarin amfani da karfi da tsarin da ba na dimokradiyya ba wajen sauya shugabanci,” a Najeriya.
A cewar Adesina, wanda bai kama suna ba, kokarin yin hakan, “haramtaccen” abu ne kuma “cin amanar kasar ne.”
“Wadannan mutanen masu son su ta da hatsaniya, suna gayyatar shugabannin wasu kabilun Najeriya da ‘yan siyasa a sassan kasar, da zimmar gudanar da wani taro, inda za a yanke kauna ga Shugaban (Buhari) - abin da ka iya haifar da hatsaniya.”
Adesina ya kara da cewa, masu yunkurin ganin an sauya gwamnatin da “karfin tuwo” suna kokari ne su aiwatar da hakan saboda gazawar da suka yi a zaben 2019.
Karin bayani akan: Femi Adesina, Facebook, Boko Haram, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
“A ranar Lahadi, hukumar tsaron farin kaya ta DSS, ta ankarar cewa, akwai wasu da ke kokarin kitsa wata makarkashiya akan gwamnatin Najeriya mai cin gashin kanta.”
Adesina ya kara da cewa, amma su kwan da sanin cewa, “fadar shugaban kasa ita ‘yan Najeriya suka dorawa ragamar tafiyar da kasar har zuwa 2023, kuma ta sha alwashin ganin ta ci gaba da hada kan kasar, ko da hakan ba zai yi wa wasu dadi ba.”
Sanarwar har ila yau ta yi gargadin cewa, “lallai a kwan da sanin cewa, akai sakamakon da ke jiran masu yunkurin cin amanar kasa.”
Wannan sanarwa da fadar shugaban kasar ta Najeriya ta fitar, na zuwa ne a daidai lokacin da wasu sassan kasar ke fuskantar matsalar tsaro da suka hada da na Boko Haram da ta kara ta’azzara a ‘yan kwanakin nan a arewa maso gabashi.
Sai kuma matsalar satar mutane da ta zama ruwan dare musamman a arewa maso yammaci, baya ga hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa a kudu maso gabashin Najeriyar.
Hakan ya sa wasu suke kira ga shugaban kasa da ya sauka a mulki ko a tsige shi, kiraye-kirayen da ya janyo ce-ce-ku-ce.
Rahotanni sun ruwaito wasu masu fada a ji a kasar da suke ba da shawarar a mika mulkin ga sojoji na dan wani lokacin don su daidaita al’amura.
Wannan kira ya sa rundunar sojin kasar ta fitar da wata sanawar a ranar Litinin, inda Kakakin hedkwatar tsaron kasar Brig. General Oyema Nwachukwu, ya nesanta sojojin Najeriya da wadannan kiraye-kiraye.
“Muna so mu tunatar da daukacin sojojinmu cewa, cin amanar kasa ne ma mutum ya yi tunanin wannan haramtaccen aiki.” Sanarwar Nwachukwu ta ce kamar yadda rahotannin suka nuna.
A cewar Nwachukwu, “bari mu fito mu fada karara, rundunonin sojin Najeriya, sun himmatu wajen marawa wannan gwamnati baya da dukkan sauran cibiyoyin dimokradiyya.”