Majalisar Dattawan Najeriya tayi afuwa tare da dawo da Sanata Abdul Ningi data dakatar a ranar 12 ga watan Maris din daya gabata.
Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar, Abba Morro ne ya fara gabatar da kudirin neman a dawo da dakataccen sanatan a yau Talatar, inda ya bayyana nadama a madadinsa.
Ya kuma sha alwashin daukar alhakin dukkanin laifuffukan Ningi, tare da bayyana girman dakatarwar.
Ayyukan sanatan sa'ilin da aka dakatar da shi sun janyo bincike da mahawara a majalisar.
Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio, ya sanar da dawo da Ningi ba tare da gindaya wani sharadi ba sakamakon rokon da wasu 'yan majalisar suka yi.
Akpabio ya jaddada mahimmanci da gudunmowar da Ningi yake bayarwa a majalisar tare da bayyana shi a matsayin dan majalisa mai mahimmancin gaske, inda yace shawarar dawo da shi ta zartar bambancin addini ko na kabila.
Majalisar ta dawo da Ningi ne ana saura makonni 2 dakatarwar da aka yi mishi ta kare a ranar 12 ga watan Yuni mai kamawa.
Dandalin Mu Tattauna