Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Wata Mashaya A Yola, Jihar Adamawa

Kungiyar Boko Haram.
Kungiyar Boko Haram.

A Najeriya kuma mun sami labarin ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene bane sun kashe mutane biyu, suka jikkata dan sanda daya da baya bakin aiki, lokacinda suka kai hari a daren jiya jumma’a a wata mashaya a unguwar Wuro Hausa dake cikin garin Yola.

Wani mutum da lamarin ya auku ba nisa daga inda yake, ya gayawa wakilin Sashen Hausa na Muriyar Amurka a Yola cewa yaji harbe harben bindiga, da yaje kuma ya tarar da gawarwakin mutane biyu, da mutum daya da aka jikkata.

Ahalin da ake ciki kuma gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana yawo na sa’o’I 24 da aka kafa a wasu kananan hukumomin jihar, yanzu an maida dokar hana yawon daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe.

Saurari:

Aika Sharhinka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG