Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Bakin Haure 21 Ne Daga Libya Suka Bace


Jirgin ruwan roban da aka ceto wasu bakin hauren
Jirgin ruwan roban da aka ceto wasu bakin hauren

Bakin haure daga Libya 21 ne suka bace bayan da wani abu ya firgitar dasu yayinda wasunsu an koma dasu Libyan kana wani jirgin 'yan kasuwa daga Cyprus ya kwashe wasu zuwa Cyprus din

Akalla bakin haure 21 daga Libya ne suka bata, kuma ake fargabar ruwa ya cinye su a yayin da suke kokarin yin bulaguro mai tsananin hatsari na tsallaka tekun Bahar Rum zuwa kasar Italiya a makon da ya gabata.

Hukumar kula da kaurar mutane ta MDD ta fada a jiya Talata cewa wadanda suka bacen suna daga cikin wasu bakin haure masu yawa da suka tashi daga Libya a cikin kwale kwalen katako da na roba wadanda aka ceto wasunsu a teku.

Wadanda suka tsira sun ce wani abu ya firgita mutane a daya daga cikin kwale-kwalen, har wasu suka fada cikin teku, amma kuma babu wani takamammen bayanin yadda abin ya faru.

Jami’an tsaron gabar tekun Libya sun dawo da wasu Libya, yayin da wani jirgin ruwan 'yan kasuwa na kasar Cyprus ya kwashe saura kuma sun isa birnin Pozzallo na kasar Italiya mai tashar jirgin ruwa jiya talata.

Adadin bakin hauren da suke kokarin zuwa nahiyar Turai daga Libya yayi kasa ainun, idan aka kwatanta da bara a daidai wannan lokaci, saboda wata yarjejeniyar da kasashen Libya da Italiay suka kulla ta mayar da irin wadannan bakin haure zuwa kasashensu, da zaran an kama su kan teku.

Jami’an hukumar kula da ayyukan kaurar mutane ta MDD, sun ce mutane 421 sun mutu yayin da suke kokarin tsallakawa zuwa Italiya a cikin wannan shekara, idan aka kwatanta da mutane 521 da suka mutu a daidai wannan loakci a shekarar 2017.

Amma kuma sun ce sama da mutane dari sun mutu a cikin irin wannan bulaguro mai hadari zuwa kasar Spain a bangaren yammacin tekun na Bahar Rum.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG