Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamhuriyar Niger Ta Fara Dawo da 'Yan Kasarta daga Libya


Bazoum Muhammad, ministan cikin gidan Niger ya tarbi wadanda suka dawo daga Libya
Bazoum Muhammad, ministan cikin gidan Niger ya tarbi wadanda suka dawo daga Libya

Biyo bayan wani rahoto da gidan talibijan na CNN dake nan Amurka ya fitar cewa ana sayar da 'yan asalin Afirka a matsayin bayi ya sa kasashe irinsu Niger fara aika jirage domin su kwasu 'yan kasarsu

Kimanin 'yan Niger 525 maza da mata dake cirani a Libya, yawancinsu matasa, suka sauka a filin jirgin saman, Yamai babban birnin kasar, da safiyar yau Alhamis.

Wannan wani yunkuri ne da gwamnatin Niger ke yi domin kubutar da 'yan kasarta dake cikin kunci a kasar Libya.

Tun farko wasu rahotanni sun bankado labarin sayar da bakaken fata a matsayin bayi a kasar ta Libya.

'Yan ciranin sun yi murnar dawowa kasarsu ta asali. Suna godiya ga Allah da gwamnatin Issoufou Mahamadou da ta tura masu jirgi domin su dawo gida.

Wasu manyan jami'an gwamnatin Niger da suka hada da Alhaji Ibrahim Yacouba ne suka je kwaso 'yan kasar.

Wadanda suka dawo suna cewa mutane na cikin wani mugun hali a ksar Libya kamar yadda tashar talibijan ta CNN ta sanarwa duniya cewa 'yan asalin kasashen Afirka ana azbtar dasu, ana tilasta masu yin aikin bayi daga karshe ko a kashesu ko kuma a sayar dasu.

Wani cikin wadanda suka dawo ya ce shi ganao ne domin ya ga ana sayar da mutane. Injishi, ya ga wadanda suke cikin mota ana tambaya ko sayar dasu za'a yi. Ya ce da zara an ga mutum baki ne to ya zama nama. Haka ma wani ya ce ya ga wadanda aka kama, da safe a yi masu duka, da yamma kuma a sake maimaita dukan.

Gwamnatin Niger tare da hukumar dake kula da 'yan cirani sun sha alwashin kwashe 'yan kasar da aka kiyasta sun fi dubu hudu a Libya domin dawo dasu.

Ministan cikin gidan kasar Bazoum Muhammad yana cikin ayarin gwamnati da suka tarbi wadanda suka fara dawowa. Ministan ya ce gwamnati zata dauki dawainiyar mayar da kowanne daga cikinsu zuwa garinsu na sali. Kana zasu aika jirage zuwa Libya sau biyar, idan kuma ta kama su kara jiragen zasu yi hakan.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG