An kwashe 'yan ci ranin kasar Somaliya da dama zuwa Mogadishu daga Libya jiya asabar cikin wani yanayi mai sosa rai.
Wadansu sun fadi a guiwoyinsu suna kuka wadansu kuma suka dungura goshinsu a kasa suna addu'a, yayinda wadansu suka rika raira taken kasar Somaliya yayinda suka sauka daga jirgin kasar Turkiya da ya daukosu daga Libya, inda wadansu suka makale na tsawon shekaru.
Tun shekara ta dubu biyu da goma sha hudu, Libya ta zama muhimmin wurin yada zango na 'yan ci rani daga kasashen Afrika da kuma gabas ta tsakiya, wadanda ke kokarin gujewa tashin hankali da nufin shiga kasashen turai.
Mataimakin firai ministan kasar Somaliya Mahdi Mohamed Guled, da 'yan majalisar dokoki da kuma wakilan kungiyoyi sun tarbi 'yan ci ranin a tashar jirgin sama. 'Yan ci rani sun bada labarin irin wulakancin da suka fuskanta da fargaba da kuma tashin hankalin da suka gani a Libya.
Facebook Forum