Dogarawan teku sun ceto mutane 86 cikin kusan mutane 150 dake cikin jirgin a tekun Meditaraniya ranar Asabar. An gano gawarwaki takwas, dukkansu na mata, ya zuwa yanzu.
Kungiyar kula da bakin haure ta duniya ta kira tekun Meditaraniya a matsayin waje mafi hatsari a duniya, bayan da bakin haure 2,832 suka hallaka a shekarar 2017, haka kuma a shekarar 2016 bakin haure 4,581 dake kokarin zuwa Italiya daga Arewacin Afirka suka rasa rayukansu.
Facebook Forum