Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayan Gwagwarmaya Majalisar Wakilan Amurka Ta Zabi Shugaba


Kevin McCarthy sabon shugaban Majalisar Dokokin Amurka
Kevin McCarthy sabon shugaban Majalisar Dokokin Amurka

Bayan kwashe zagaye 15 ana kada kuri'a cikin kwanaki biyar ga dan jam'iyyar Republican mai sausaucin ra’ayi, daga karshe an zabi Kevin McCarthy a matsayin kakakin majalisar wakilan Amurka a yau Asabar.

Shugaban Amurka Joe Biden ya fitar da wata sanarwa ya na taya McCarthy murna, yana mai cewa, "Na shirya yin aiki tare da 'yan Republican lokacin da zan iya, kuma masu jefa kuri'a sun bayyana karara cewa suna sa ran 'yan Republican su kasance cikin shirin yin aiki da ni su ma."

Da yammacin ranar Juma’a, bayan kada kuri’a karo na 14 an yi yunkurin dage zaman majalisar har zuwa ranar litinin, amma hakan bai yiwa ba bayan da ‘yan jam’iyyar Republican suka sauya salo tare da yanke shawarar yin wani yunkuri na 15 na zaben sabon shugaban.

Wasu gungun 'yan majalisa 20 na masu ra’ayiin rikau sun hana McCarthy samun nasara a zabukan da suka gabata saboda sun yi imanin cewa ba zasu zabe shi ba.

A wata arangama da ba a saba gani ba, McCarthy ya yi musayar kalamai da wakilin jam’iyyar Republican Matt Gaetz na Florida a benen zauren majalisar, bayan kada kuri’a karo na 14 saboda dan majalisar ya kada kuri’ar wata kuri’a maimakon kada kuri’ar da za ta bai wa McCarthy damar zama shugaban majalisar.

Dan jam’iyyar Republican bai taba bayar da wata alamar cewa zai fice daga takarar neman shugabancin majalisar ba, wanda kuma bisa tanadin kundin tsarin mulkin Amurka, zai sa ya zama mutum na biyu a jerin wadanda za su iya maye gurbin shugabancin Amurka.

XS
SM
MD
LG