Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Kakakin Majalisar Wakilan Amurka: McCarthy Ya Sake Faduwa A Zagaye Na Hudu


Kevin McCarthy, hagu
Kevin McCarthy, hagu

A ranar Talata majalisar ta kada kuri’a sau uku ba tare da samun nasara ba, lamarin da ya kai ga aka dage zaman zuwa Laraba.

Shugaban ‘yan Republican a majalisar wakilan Amurka Kevin McCarthy, ya sake gaza samun kuri’un da za su ba shi damar zama kakakin majalisar.

Wannan shi ne karo na hudu da ake kada kuri’a amma McCarthy ya gaza kai wa ga gaci.

A ranar Talata majalisar ta kada kuri’a sau uku ba tare da samun nasara ba, lamarin da ya kai ga aka dage zaman zuwa Laraba.

McCarthy na bukatar ya samu kuri’a 218 kafin ya samu nasara, kuma ga dukkan alamu, har yanzu, wasu ‘yan Republican da yawansu ya kai 20, sun ki sauya matsayarsu.

Dukkan ‘yan Democrat 212 da suka kasance masu karamin rinjaye a majalisar, sun zabi Hakeem Jefferies a matsayin dan takararsu.

McCarthy wanda ke wakiltar jihar California ya sha alwashin cewa zai ci gaba da fafatawa ko da sau nawa za a je zabe.

A wannan karon ‘yan Republican din da suke boren zaben McCarthy, sun jefawa dan Republican Bryan Donald kuri’unsu ne.

Rabon da majalisar ta gaza zaben shugabanta a zagayen farko tun a shekarar 1923.

Wannan rikata-rikitar siyasa da ta mamaye majalisar dokokin Amurkar, na nuni da irin jan aikin da ke gaban ‘yan Repiblican da suka karbe ikon majalisar wakilan.

Yanzu ya zama dole sai an sake yin zabe a zagaye na biyar.

Bisa tsarin doka, majalisar ba za ta fara gudanar da ayyukanta ba har sai an zabi kakaki. Wanda aka zaba, shi zai maye gurbin Nancy Pelosi.

XS
SM
MD
LG