WASHINGTON DC - A jiya Alhamis, jami'an Hukumar Zaben Afrika ta Kudu suka tsame sunan tsohon shugaban kasar Jacob Zuma daga jerin wadanda zasu tsaya zabe a watan Mayu mai zuwa, abinda ya kara dumama yanayin siyasar kasar gabanin zaben.
Afrika ta Kudu zata gudanar da babban zabenta a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa, zaben da ake sa ran ya zama mafi fafatawa a yakin neman kuri'u tun bayan fara mulkin dimokradiya a kasar a shekarar 1994.
Jam'iyyar ANC mai mulkin kasar na daf da yin asarar fiye kaso 50 cikin 100 na kuri'unta a karon farko tun bayan data hau kan karagar mulki a karshen mulkin wariyar launin fatar kasar.
Jam'iyyar na cigaba da asarar magoya baya sakamakon raunin tattalin arziki da zarge-zargen cin hanci da rashawa da rashin iya mulki.
A shekarar 2018 ne zarge-zargen cin hanci da rashawa suka hambarar da Jacob Zuma mai shekaru 81 daga kan karagar mulki, amma har yanzu yana da tasiri a siyasar kasar.
Zuma ya jima yana yiwa jam'iyyar MK me hamayya kamfe, tare da kiran 'ya'yan tsohuwar jam'iyyarsa ta ANC da maciya amana a wani yunkuri na komawa kan kujerarsa.
Dandalin Mu Tattauna